Zuwa yanzu hukumomin lafiya a Najeriya sun yi wa fiye da mutum miliyan daya rigakafin kariya daga annobar korona.
Hukumar lafiya matakin farko ta fitar da alkaluman rigakafin na yi wa mutum 1,081,548 da hakan ya nuna an yi wa kashi 53.8% na mutane a rukunin farko na rigakafin.
In za a tuna an samu kimanin allurai miliyan hudu daga kason tallafi na COVAX da ke tallafawa kasashe masu tasowa na alluran AstraZeneca.
Akalla an samu wasu da su ka yi kukan zazzabi mai zafi bayan yin rigakafin.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Good day! Do you use Twitter? I’d like to follow you if that would be ok.
I’m definitely enjoying your blog and look forward
to new updates.