Zuwa yanzu alkaluma sun nuna mutum 42 ne su ka rasa ran su a sanadiyyar rugujewar ginin Ikoyi a Lagos.
In za a tuna, ginin mai hawa 21 ya ruguje da sanadiyyar mutuwar mutane ciki har da wadanda ke kwangilar aikin Femi Osibona.
Gwamnan Lagos Babajide Sanwo Olu ya ce kazalika mutum 15 su ka tsira daga hatsarin.
Olu na magana ne a gaban ginin da rakiyar uban APC Bola Tinubu da kuma gwamnan jihar Nassarawa AA Sule.
An samu adadin iyali 49 da su ka baiyana cewa hatsarin ya rutsa da ‘yan uwan su.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀