Zuwa yanzu hukumar gidajen yarin Najeriya ta ce an sake cafke wasu daga cikin ‘yan gidan yarin Jos da su ka arce sakamakon harin da ‘yan bindiga su ka kai kan gidan yarin.
Kamfanin dillancin labarun Najeriya NAN ya ruwaito cewa zuwa yanzu an cafke mutum 21 cikin mutum 262.
Tun farkon kai harin da ‘yan yarin su ka arce an ba da labarin sake cake 10 daga ciki inda a ka cigaba da neman sauran.
Wannan dai ya nuna yanzu akwai sauran mutum 239 da a ke nema.
Hukumar gidan yarin ta baiyana daukar matakan hana fasa gidan yari a Najeriya da ya faru a jihohi kusan 3 koma fiye da haka.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀