• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZUBAR DA JINI-SIMON LALONG YA YI WA SHUGABA BUHARI BAYANI

Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayani kan yanda a ke samu fitina a jihar sa da kan yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiya.

Gwamnan Lalong ya yi alwashin duk masu hannu a fitinar za su dandana kudar su.

Gwamnan dan APC mai mulki a taraiya wanda ya ke wa’adin sa na biyu kan mulki, ya ce ba zai bari wasu miyagun iri su bata kokarin da a ka yi na tsawon lokaci na wanzar da zaman lafiya ba.

Lalong ya ce duk masu fitinar za a gurfanar da su gaban kotu don su fuskanci hukunci kan laifin da su ka aikata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnati za ta tallafawa wadanda lamarin ya shafa ta hanyar hukumar tallafin jinkai.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.