• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZUBAR DA JINI A FILATO MUGUN LAIFI NE-BASARAKEN IBAAS

Basarake daga yankin barikin Ladi a Jihar Filato Gwom Ibaas ya ce zubar da jini a jihar Filato mugun laifi ba da ke maida hannun agogo baya a jihar.

Basaraken Dr.Luka Pagyang Pam na zantawa ne da kafar labarun ketare Abuja inda ya ce a baya Filato waje ne na neman arziki amma yanzu wasu na nema kawo cikas ga jihar mai arzikin noma da kiwo.

Ibaas Gwom ya kara da cewa kisa da fakewa da bambancin addini ko kabilanci son zuciya kawai don ba wata ka’ida da ta koyar da hakan.

Mai sarautar ya bukaci gwamnati ta karawa sarakuna karfi ba sai ta jira an samu fitina ba kafin gaiyatar su don samu bakin zare.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.