• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZIYARAR YARIMA MUHAMMAD BIN SALMAN A DOHA TA KARA RAGE RASHIN JITUWA TSAKANIN KASASHEN BIYU

ByNoblen

Dec 10, 2021 ,

Ziyarar da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bin Salman a kasar Katar ta taimaka wajen rage mummunar rashin jituwa tsakanin kasashen larabawan biyu.
In za a tuna a zamanin mulkin Donald Trump na Amurka, Katar ta so nuna da Saudiyya ta yi amfani da biliyoyin dalar Amurka na yarjejeniya da Amurka kan wasu lamuran daban; inda hakan ya fusata Saudiyya da daukar hakan a matsayin raini da shishshigi.
Saudiyya ta rufe Katar da daukar matakan karya tattalin arzikin ‘yar karamar kasar ta larabawa mai amfani da tashar ta ta talabijin ALJAZEERA wajen yada farafaganda.
Tun yarjejeniyar zama a birnin Al’ula na Suadiyya, a ke cigaba da samun ingantar danganta tsakanin kasahen, kuma saukar Yarima Muhammad a birnin Doha shi ya zama babbar alamar hakan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *