• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZIYARAR SHUGABA BUHARI ZUWA DAURA BA TA SAUYA BA

ByNoblen

Jul 6, 2022

Ziyarar shugaba Buhari zuwa mahaifar sa Daura ba ta sauya ba don tawagar sharer fage ta ma’aikatan shugaban na cigaba da shirye-shiryen tarbar sa kamar yanda a ka saba.

Wannan dai ya kwantar da sharhin tunanin ba mamaki shugaban ya janye tafiyar biyo bayan arangama da tawagar jami’an sa daga fadar Aso Rock ta yi da barayin daji kan hanyar tafiya Daura.

Rahotanni na baiyana cewa garin Daura dai na nan kamar yanda a ka saba da masu tarar shugaban kasa wadanda su ka tsira ko tsallake rijiya da baya a kan hanya da barayin daji ke cin karen su ba babbaka.

Daya daga ‘yan jaridar fadar Aso Rock Hassan Umar Farouk da ke Daura don dauko rahotannin ziyarar, ya ce duk tawagar na lafiya in ka debe mutum biyu da su ka samu rauni.

Hassan Farouk da ke aiki da kafar labaru ta LIBERTY ya ce shi da sauran ‘yan jarida sun shirya tsaf don zantawa da shugaban a ranar sallah.

Dan kamfen shugaba Buhari da ya yi aiki a sashen shirye-shirye Magaji Muhammad Yaya ya ce harin wani sako ne na farkar da shugaba Buhari da gwamnatin sa yanda lamuran tsaro su ka tabarbare.

Bayan gani da ido da shugaba Buhari ya je gidan yarin Kuje da ‘yan bindiga su ka kai wa hari, zai zarce Dakar din Senegal don ziyarar aiki kafin daga can ya shigo Daura.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.