• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZIYARAR SHUGABA BUHARI GA TINUBU NA NUNA TINUBUN YA YI JINYA

Ganin hoton ziyarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai wa uban jam’iyyar APC Bola Tinubu a London,  na nuna Tinubun ya yi jinya.

Kazalika shi kan sa shugaba Buhari wanda ya duba likitan sa a London, ya nuna murmurewa daga hoton da ya dauka da Tinubu.

Bayanan sun nuna ziyarar ta auku ne a gidan Tinubun da ke London.

Abu biyu sun baiyana daga hoton ziyarar :

1.Tinubu ya yi jinya ba kamar yanda jami’in labarun sa ke cewa ya yi tafiya kawai ketare ba kuma tamkar ba abun da ya same shi.

2.Hakan ya nuna Tinubu na nan da ran sa sabanin labarin da wasu su ka yada cewa ya mutu ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *