Rahoto ya tabbata da ke nuna gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya karbi sunayen wadanda a ka tantance don cankar sabon Sarkin Zazzau a cikin su.
Bayanai dai na nuna za a tura sunayen don gudanar da bincike kan tarihin lamuran tsaro da karin cancanta.
Daga bayanai da a ka samu na nuna akwai sunayen mutum 3 da a ka tantance da su ka hada da Iyan Zazzau Alhaji Bashir Aminu, Yariman Zazzau Alhaji Munir Jafaru da Turakin Zazzau Alhaji Aminu Shehu Idris.
Jinkirin kamar yanda a ka fahimta daga sakataren gwamnatin Kaduna Alhaji Balarabe Abbas Lawal ba ya rasa nasaba da dadewa da a ka yi ba a samu aiki da tsarin nada Sarkin Zazzau ba tun gudanar da hakan a 1975 lokacin da Sarkin Zazzau Aminu ya rasu a ka nada marigayi Shehu Idris.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀