Jaridar Daily Trust ta ce ta fahimci cewa yanzu an kara sunan mutum daya cikin wadanda a ka tantance don zabar daya daga cikin su ya zama Sarkin Zazzau. Biyo bayan kara sunan na hannun daman gwamna El-rufai wato Magajin Garin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, yanzu jerin sunayen ya zama mutum 4.
Wadanda tun farko a ka mika sunan su ga gwamna El-rufai sun hada da Iyan Zazzau Alhaji Bashir Aminu, Yariman Zazzaau Alhaji Munir Jafaru da Turakin Zazzau Alhaji Aminu Shehu Idris.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀