• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZAUREN VOA ABUJA ZAI ZANTA KAN ZULLUMIN KARA FARASHIN MAN FETUR

Taron masana kan fannoni da Muryar Amurka kan gabatar a wata-wata a ofishin ta da ke Abuja mai taken “ZAUREN VOA” a asabar din nan 15/01/2022 zai tattauna kan zullumin da talakawan Najeriya ke ciki kan muradin gwamnatin Najeriya na kara farashin man fetur.
Tun baiyana shirin janye dukkan tallain fetur da shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari Kolo ya yi, jama’a ke ta sharhi inda akasarin su ke fatar gwamnati za ta sake tunani.
Bayanan Kolo da ke nuna janye tallafin ka iya cilla litar fetur zuwa Naira 320-340 ya tayar da hankalin talakawa don yanzu haka ma da litar ke wajajen Naira 162-165 muhimman kayan masarufi na da dan Karen tsada.
Masu ruwa da tsaki daga sashen fetur, jami’an kwadago da sauran jama’a talakawa za su halarci zaman don baiyana matsayar su kan lamarin da ke tinkarowa.
Hakika karin farashin fetur da tashin farashin dalar Amurka na kan gaba a dalilan da kan kawo kuncin rayuwa a Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
13 thoughts on “ZAUREN VOA ABUJA ZAI ZANTA KAN ZULLUMIN KARA FARASHIN MAN FETUR”

Leave a Reply

Your email address will not be published.