• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZARGIN KASHE KHASHOGGI-AN SAKO KHALID AL-OTAIBI YA KOMA HANYAR DAWOWA SAUDIYA DAGA FARANSA

ByNoblen

Dec 9, 2021 ,

Hukumomi a Faransa sun sako dan Saudiyya da su ka kama mai suna Khalid Al-Otaibi da a ka yi wa zargi da kashe dan jaridar nan Jamal Khashoggi.
Rike Al-Otaibi ya zama kanun labaru musamman don tuhumar sa da kashe Khasoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul a Turkiyya.
Jami’ai a Faransa sun ce an yi kuskuren kama Al-Otaibi don sunan sa ne ya zo daya da Al-Otaibi da a ke zargi da kashe Khashoggi.
Ofishin jakadancin Saudiyya a Faransa ya tabbatar an sako Al-Otaibi inda ya kamo hanyar dawowa gida.
Saudiyya ta baiyana cewa dukkan masu hannu 11 kan kashe Khashoggi an yanke mu su hukunci inda 5 daga ciki a ka yanke mu su hukuncin kisa, 3 daga ciki an yanke mu su hukuncin dauri na wa’adi daban-daban inda sauran ukun a ka sake su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *