• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZANGA-ZANGA: AN JEFI KWAMBAR MOTOCIN GWAMNAN

An jefi motocin gwamnan jihar Osun Gboyega Oyetola a wajen zanga-zangar kawo karshen ‘yan SARS a birnin Oshogbo.
Oyetola ya sanya alamun zanga-zanga ya iso dandali inda masu zanga-zangar su ka nemi sai ya nemi ahuwar rashin zuwa tun da a ka fara fitowa inda shi kuma ya nemi ahuwar.

Gwamnan ya na tsakiyar jawabi sai wasu su ka dinga Ihu inda daga bisani a ka ji karar harbe-harbe.

Da kyar gwamna ya kutsa a kwambar motocin ya fice daga turmutsutsun.
An gobje motar gwamnan da makamai inda ya samu ya arce zuwa tudun mun tsira.

Ra’ayin jami’an gwamnatin jihar shi ne an kai hari ne don hallaka gwamnan da wasu miyagun iri da su ka shigo rigar zanga-zanga su ka yi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ZANGA-ZANGA: AN JEFI KWAMBAR MOTOCIN GWAMNAN”
  1. It’s really a nice and useful piece of info. I’m happy that you shared this helpful info with us.

    Please stay us informed like this. Thank you for sharing.

Leave a Reply

Your email address will not be published.