A sabuwar zanga-zangar fusata da juyin mulkin soja a Sudan, akalla mutum 5 su ka rasa ran su a yunkurin jami’an tsaro na tarwatsa jama’ar da su ka fantsama kan tituna.
Tun kwace gwamnatin mika mulki ga farar hula ta Mustapha Hamdok, a ke samun zanga-zanga da suka daga wasu kasashen duniya.
Mutane sun sake sabon yunkuri ta hanyar fitowa kan titunan babban birnin kasar Khartoum da tagwayen sa na Oumdurman inda sojoji su ka bude wuta har a ka samu asarar rayuka da kuma samun raunuka.
Shugaban mulkin sojan kasar Janar Abdelfattah Burhan ya ce sun dau matakin kawar da fararen hular ne don kare muradun kasar Sudan.
Burhan ya ce shirin maida mulki hannun farar hula da ya biyo bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaba Omar Elbashir na nan.
ZANGA-ZANGA A SUDAN- MUTUM 5 SUN RASA RAN SU

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
As the admin of this web page is working, no question very shortly it will be renowned, due
to its feature contents.
I think this is among the most vital info for me. And i am glad reading your article.
But want to remark on few general things, The website style is
perfect, the articles is really great : D. Good job, cheers