• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZAN TABBATAR AN AMINCE DA SABON TSARIN MULKI KAFIN NA KAMMALA SABON WA’ADI-ADAMA BARROW

Shugaban Gambia Adama Barrow wanda ya zarce kan mulki, ya ce zai tabbatar an amince da sabon tsarin mulkin kasar kafin ya kammala sabon wa’adin san a shekaru 5.
Barrow ya fara zama shugaban Gambia a 2016 bayan takaddamar zabe da tsohon shugaban kasar Yahaya Jammeh wanda ya share fiye da shekara 20 kan mulki.
Adama Barrow ya kawo sabon tsarin mulki don maye na kasar na 1997 amma majalisa ba ta amince da shi ba.
A cikin sabon tsarin mulkin akwai tanadin shugaban kasar zai iya yin shekaru 5 sau biyu ya na mulki wato wa’adi biyu na shekaru 10.
Yanzu dai ba tabbas in an amince da sabon tsarin mulkin, ko kidayar mulkin Barrow za ta fara daga wa’adin sa na farko ko za a yi sabon lissafi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.