• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZAN SANAR DA SABUWAR JAM’IYYAR DA ZAN SHIGA-JIBRIN

Jagoran kamfen din neman shugaban kasa na Bola Tinubu wato Abdulmumin Jibrin ya baiyana cewa zai shiga wata jam’iyya nan gaba kadan.

Ba mamaki Jibrin wanda ya kai ruwa rana da tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara amma bai cimma nasara ba, bai samu alamun yin takara ba ne a APC.

Kazalika hakan na nuna ya zama wajibi a gare shi ya bar tafiyar ta Tinubu ko kuma za a iya cewa daman kamar shi ya dage da zama kan mukamin.

Ko wace jam’iyya dan takara zai shiga sai ya yi kan lokaci kasancewar hukumar zabe na nuna ba za ta tsawaita lokacin karbar sunayen ‘yan takara ba a makwan farko na watan gobe.

Jam’iyyu dai a halin yanzu na dabarun kula da matsalolin juna don cin gajiyar hakan ta hanyar sauya sheka da wadanda ba su ji dadi ba za su yi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.