• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZAN MURKUSHE BARAYIN DAJI- INJI SHUGABA BUHARI BAYAN FUSATA DA YAWAN ZUBAR DA JINI

ByYusuf Yau

Oct 19, 2021
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya lashi takobin murkushe barayin daji biyo bayan sabbin hare-hare da su ka haddasa asarar rayuka.
Shugaban ya yi matukar fusata da yanda ‘yan bindigar su ka shiga kasuwar Goranyo a jihar Sokoto inda su ka yi kisan gilla ga akalla mutum 30.
Shugaban a sanarwa daga mai taimaka ma sa kan labaru Garba Shehu, ya ce dubun ‘yan bindigar ya na gab da cika don za a yi mu su dirar mikiya.
Sanarwar ta ce ‘yan bindigar na cikin dimauta don yanda a ka kai mu su farmaki ta jiragen sama da kuma dakarun kasa.
Shugaban ya bukaci ‘yan Najeriya kar su samu karayar zuciya don gwamnati na kan bakanta na kare rayuka da dukiyoyin su.
Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “ZAN MURKUSHE BARAYIN DAJI- INJI SHUGABA BUHARI BAYAN FUSATA DA YAWAN ZUBAR DA JINI”
  1. Pretty nice post. I just stumbled upon your blog and wished to say that I have really enjoyed browsing your blog posts. In any case I will be subscribing to your feed and I hope you write again soon!

Leave a Reply

Your email address will not be published.