• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZAN MARA BAYA GA WADANDA ‘YAN NAJERIYA SU KA ZABA NE-SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari y ace zai mara baya gad an takarar da ‘yan Najeriya su ka zaba ne a 2023.
Shugaban na amsa tambaya ne kan ko waye ya ke sha’awar marawa baya a babban zaben mai zuwa yayin da zai kammala wa’adin sa na biyu.
Gabanin wannan sabuwar matsaya, shugaban ya baiyana cewa ba zai baiyana sunan wanda ya ke son marawa baya ba don kar a shiryawa dan takarar na sa makarkashiya.
Ba mamaki shugaban na nufin kowa ye ya lashe zabe ko ba daga jam’iyyar sa ta APC ba ne zai mika ma sa ragama.
Kazalika a sakon san a sallah, shugaban ya ba da tabbacin ba da goyon baya don=gudanar da zabe nagartacce.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ZAN MARA BAYA GA WADANDA ‘YAN NAJERIYA SU KA ZABA NE-SHUGABA BUHARI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.