• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZAN HALLAKA DALIBAN JAMI’A DA MU KA KWASHE-MADUGUN BARAYIN DALIBAI JAMI’AR GREENFIELD

Shugaban gungun barayin da su ka sace daliban jami’ar Greenfield a Kaduna Sani Idris Jalingo da a ka fi sani da “BALERI” ya yi barazanar hallaka sauran dalibai matukar ba a turo ma sa fansar Naira miliyan 100 da baburan Boko Haram 10 ba.

Baleri a zantawa ta wayar tarho daga daji inda ya ke tsare da daliban 17 bayan kashe 5 daga ciki, ya ce ranar talata zai dau mummunan matakin matukar ba a turo sakon ba.

Baleri wanda ke nanata cewa da gaske ya ke yi wajen barazanar, ya baiyana cewa yanzu haka akwai mata 15 da maza biyu a hannu su da su ka hada da jikan marigayi sarkin Zazzau Shehu Idris mai suna Hamza.

Yayin da Baleri ke cewa iyayen yaran sun turo mu su diyyar da ta kai naira miliyan 55, ya ce sun sassauto daga wajen Naira miliyan 600 da su ka nema tun farko, yanzu su na bukatar miliyan 100 kuma sun yi amfani da kudin da a ka fara turowa wajen sayawa yaran garin kwaki.

An zanta da daya daga yaran Hamza wanda ya bukaci a kawo mu su daukin gaggawa.

Ita ma daya daga daliban mata Abigail Usman ta ce kar a dauki barazanar barayin da gangan.

Madugun barayi Baleri ya ce wannan shi ne wa’adi na karshe da zai bayar na yau litinin din nan.

Har yanzu akwai daliban kolejin kimiyyar gandun daji da ke hannun wasu gungun barayin da hakan ya maida jihar Kaduna mafi fama da kalubalen barayin mutane.

Gwamnatin Kaduna na nanata ba ta mara baya ga biyan fansa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “ZAN HALLAKA DALIBAN JAMI’A DA MU KA KWASHE-MADUGUN BARAYIN DALIBAI JAMI’AR GREENFIELD”
  1. These are actually great ideas in about blogging.

    You have touched some fastidious factors here.
    Any way keep up wrinting.

Leave a Reply

Your email address will not be published.