• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZAN CIGABA DA SIYASAR BABA NA RAFIK HARIRI DON CETO LEBANON-BAHAA HARIRI

ByNoblen

Jan 29, 2022 ,

Yayan tsohon firaministan Lebanon Saad wato Bahaa Hariri ya samu sabanin ra’ayi da kanin sa kan shiga zaben majalisar dokokin kasar.
Tun farko Saad Hariri ya ce ba zai shiga zaben majalisar dokokin kasar ba, kuam ya bukaci jam’iyyar sa ma kar ta shiga.
In za a tuna a 2005 a ka kai harin bom kan kwambar motocin mahaifin su Rafik Hariri da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar sa.
Bagaren su Rafik ne ke da tagomashi a tsaknin musulmi ‘yan ahlussunnah a Lebanon.
Bahaa mai shekaru 55 ya ce shi zai shiga zaben kuma tunanin an samu sabani a bangaren ‘yan siyasar ahlussunnah tunai ne kawai na magaoya bayan Iran da ke shigowa Lebanon ta hanyar kungiyar Hezbollah ta ‘yan shi’a.
Lebanon a siyasance na da tsarin shugaban kasa ya fito daga ‘yan shi’a, shugaban majalisar dokoki daga ‘yan shi’a sai firaminista ya fito daga ahlussunnah.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
21 thoughts on “ZAN CIGABA DA SIYASAR BABA NA RAFIK HARIRI DON CETO LEBANON-BAHAA HARIRI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.