Sanadiyyar tattaunawa da madugun barayi a jihar Zamfara, ya sa barayin kyale mazauna kauyukan yankin Shinkafi komawa gidajen su.
Madugun barayin mai suna Turji ya yi fushi ne don zargin mutanen kauyukan da fallasa aiyukan barayin, inda hakan ya kai ga jami’an tsaro su ka cafke mahaifin sa a kan iyakar Kano da Jigawa.
Turji ya ce da shi ya kamata a yi wa dirar mikiya tun da shi a ke nema amma ba mahaifin sa da ya ce ba shi da laifi ba.
Tun gabanin sulhun, Turji ya tada mutane daga garuruwan su da kuma sace fiye da mutum 50.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Hi i am kavin, its my first occasion to commenting anyplace,
when i read this piece of writing i thought
i could also make comment due to this good post.