• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZAMAN ZULLUMI YA KARU A KASAR UKRAINE DON YIWUWAR MAMAYE KASAR DAGA SOJOJIN RASHA

A na zaman zullumi a kasar Ukraine don yanda alamu ke nuna kasar Rasha na shirye-shiryen mamaye kasar.
Karin alamun sun baiyana biyo bayan umurnin da Amurka da ita kan ta Rasha su ka yi wa wasu daga jami’an jakadancin su, su fice daga babban birnin kasar Kyiv.
Kakakin ma’aikatar wajen Rasha Maria Zakharova ta baiyana cewa fargabar daukar matakin fusata daga hukumomi Kyiv ko wasu kasashe ya sa Rasha ta ke rage jami’an ta na diflomasiyya a kasar.
Ita ma Amurka ta dau irin wannan mataki na bukatar jami’an ta da ban a wajibi ba su fice daga Kyiv don kar shirin mamayar Rasha ya rutsa da su.
Ma’aikatar wajen Rasha ta ce sakataren harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a zantawa ta wayar tarho da sakataren wajen Amurka Anthony Blinken, ya zargi Amurka da yada farafaganda kan batun cewa Rasha za ta mamaye Ukraine.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ZAMAN ZULLUMI YA KARU A KASAR UKRAINE DON YIWUWAR MAMAYE KASAR DAGA SOJOJIN RASHA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.