• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZABEN ‘YAR TINKE A FIDDA TAKARAR JAM’IYYU NE YA FI SAHIHANCI-MUSA ABUBAKAR DANMALIKI

ByNoblen

Nov 26, 2021

‘Yan siyasa da dama na mara baya ga kudurin dokar nan da majalisar dokokin Najeriya ta sanyawa hannu kuma a ka mikawa shugaba Buhari don sanya hannu ya zama doka.
Dan kwamitin tallafawa zaben shugaba Buhari PSC Alhaji Musa Abubakar Danmalikin Kebbi ya ce wannan doka za ta taimaka ainun wajen dakile dauki-dora na ‘yan takara da ke faruwa a jam’iyyu bisa karfin wasu masu karfin fada aji ko ba a son ji.
Danmalikin Kebbi ya ce masu adawa da kudurin na son cigaba da kawo magudi a lamuran tsayar da ‘yan takara da hakan ke haddasa bullowar shugabanni da ba su da goyon bayan Jama’a sai wadanda su ka nada su.
Tuni dai majalisar ta mika kudurin ga shugaba Buhari da a sa ran sanya hannun sa, duk da raderadin cewa gwamnoni na kulla wata dabarar hana kudurin dokar samun nasara.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “ZABEN ‘YAR TINKE A FIDDA TAKARAR JAM’IYYU NE YA FI SAHIHANCI-MUSA ABUBAKAR DANMALIKI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.