• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZABEN ONDO – BABBAN SUFETON ‘YAN SANDA YA TURA DIG, AIG DA KWAMISHINONI 11

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya tura mukaddashin sa daya, mataimakin sa daya da kwamishinoni 11 don kula da tsaro a zaben gwamnan jihar Ondo da za a gudanar ranar asabar 10 ga watan nan na nuwamba.

Wannan dai tamkar kara yawan jami’an ne in a ka kwatanta da wadanda a ka tura kula da zaben gwamnan jihar Edo. Manyan jami’an da su ka kula da zaben Edo su ne a ka sake turawa wato DIG Adeleye Olusola Oyabade da AIG Karma Hosea Hassan.

Sanarwar ta gargadi jami’an tsaro da ke raka manyan ‘yan siyasa kar su raka su a ranar zaben. Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya tsaya takarar don neman wa’adi a inuwar APC inda Eyitayo Jegede ke yi wa babbar jam’iyyar adawa PDP takarar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.