• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZABEN FIDDA GWANI-BA A SAN MACI TUWO BA

Zuwa yanzu ‘yan takarar mukamai musamman na shugaban kasa da gwamnoni na kara takarkarewa wajen neman goyon bayan wakilan zaben na jam’iyyun su don samun tagomashi a zaben na fidda gwanaye.

Duk ba mamaki a wasu jam’iyyun a ka iya jingine wakilan a daidaita wajen tsayar da ‘yan takara, hakan bai dakatar da ‘yan takara masu himma yawo duk inda su ke tunanin yin gamo da magoya baya ba, a yanayin “ba a san maci tiwo ba sai miya ta kare.”

Da alamu wasu ‘yan takarar shugaban kasa na himmar zagaye jihohi 36 na kasar da Abuja don nuna su ne su ka fi cancanta a zaba.

An lura da kashe makudan kudi wajen shatar jirage don wannan yawo da sam ba zai yi nasara ta kan tituna ba.

A na samun wasu gwamnoni da kan fito karara su baiyana dan takarar shugaban kasa da za su marawa baya da hakan ke nuna za a fafata a zabukan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
5 thoughts on “ZABEN FIDDA GWANI-BA A SAN MACI TUWO BA”
  1. Hello! I could have sworn I’ve been to this blog before but after browsing through some of the post I realized it’s new to me. Anyways, I’m definitely happy I found it and I’ll be book-marking and checking back frequently!

Leave a Reply

Your email address will not be published.