• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZABEN AMURKA: ‘YAN TAKARA SUN MAIDA HANKALI A KAN JIHOHIN RABA-GARDAMA

Yayin da babban zaben Amurka ke karatowa a ranar 3 ga watan gobe, manyan ‘yan takara shugaba Donald Trump da Joe Biden sun maida hankali kan jihohin raba-gardama maimakon biyewa yawan kuri’u.
Jihohin raba gardama masu yawan cibiyoyin zabe su 7 don haka maida hankali kan su na da muhimmanci.

Hakan na nuna ba yawan kuri’a ke sa dan takara lashe zaben Amurka ba amma lashe zabe a wadannan jihohin.
In za a tuna a 2016 ‘yar takarar Dimokrats Hillary Clinton ta samu kusan kuri’a miliyan uku sama da na Donald Trump, amma hakan bai sa ta lashe zaben ba.

Alkaluman da kafafen labaru ke yadawa na nuna Joe Biden zai fi samun yawan kuri’u, amma ba za a tantance yanda lamarin zai kaya a sakamakon zaben jihohin raba-gardama ba.
Jihohin masu muhimmanci sun hada da Iowa, Pennsylvania,  Florida, Michigan, Wisconsin, Ohio da North Carolina. 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “ZABEN AMURKA: ‘YAN TAKARA SUN MAIDA HANKALI A KAN JIHOHIN RABA-GARDAMA”
  1. Your means of explaining the whole thing in this paragraph is actually good, all be capable of simply understand it,
    Thanks a lot.

  2. Attractive part of content. I just stumbled upon your website and in accession capital to assert that I acquire actually enjoyed account your
    weblog posts. Any way I’ll be subscribing on your feeds or even I
    fulfillment you get admission to consistently quickly.

Leave a Reply

Your email address will not be published.