• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZABEN AMURKA: SHUGABAN BUHARI TAYA BIDEN MURNA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shiga jerin wasu shugabannin duniya wajen taya Joe Biden nasarar lashe zaben Amurka da samun rinjaye a kuri’un jihohin raba gardama.

Shugaban na Najeriya ya nuna Biden ya samu nasarar daidai lokacin da duniya ke cikin wani yanayi na kalubale.

Hakanan Shugaba Buhari ya nuna muhimmancin dimokradiyya da kan ba wa mutane dama su zabi wanda zai jagorance su ta hanyar sauya gwamnati cikin ruwan sanyi.

A cewar shugaba Buhari, ba ‘yan siyasa ne ajin mutanen da su ka fi karfi ba, amma masu zabe ne su ka fi karfi.

Shugaba Buhari ya ce ya yi farin ciki da nasarar Biden don kasancewar Biden dan majalisa na shekaru 40 kafin zama mataimakin shugaban kasa na tsawon shekaru 8 zamanin mulkin Barrack Obama.

Ba za a yi mamakin wannan matsaya ta shugaba Buhari ba, in an duba irin jituwar sa da tsohon shugaban Amurka Barrack Obama gabanin ya hau mulki a 2015.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ZABEN AMURKA: SHUGABAN BUHARI TAYA BIDEN MURNA”
  1. I read this piece of writing fully concerning the comparison of hottest and previous technologies, it’s
    amazing article.

Leave a Reply

Your email address will not be published.