• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZABEN 2023-SHUGABA BUHARI YA GANA DA GWAMNONIN APC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin jam’iyyar sa ta APC kan zaben fidda gwani na jam’iyyar da za a gudanar ranar litinin da talata mai zuwa.

Ganawar wacce ta gudana a fadar Aso Rock ta samu halartar shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu.

Shugaban ya bukaci gwamnonin su taimaka ma sa wajen samun kwakkwaran dan takarar da zai yi tasiri a zaben.

Hakanan shugaban ya nuna duk wanda zai samu takarar ya dace ya zama ya na da dabarun inganta lamuran Najeriya.

APC na da mafi yawan gwamnoni a Najeriya inda PDP ke mara ma ta baya.

Rashin fahimta ta cikin gida tsakanin gwamnonin da wasu jiga-jigan jam’iyyar na haddasawa jam’iyyar cikas duk da batun sulhu da ba mamaki ya zama na ciki na ciki.

APC wacce ta jinkirta gudanar da zaben fidda gwani zuwa makwan nan, ta shiga tsaka mai wuya na tsayar da dan takara daga arewa ko kudu musamman bayan nasarar Atiku a zaben fidda gwani na PDP.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.