Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika takardar bukatar karbo karin lamuni na dala biliyan 4 da kuma fam miliyan 710.
Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan ya gabatar da takardar bukatar gaban majalisar don amincewa.
Bayanan bukatar sun nuna bankin duniya, Cibiyar lamuni ta Faransa da bankin NEXIM ne za su samar da kudin.
Shugaba Buhari ya ce za a yi amfani da kudin don aiwatar da aiyukan da majalisar sa ta zartarwa ta amince da su zuwa watan Yunin da ya gabata.
Wannan ba shi ne karo na farko da gwamnatin ke neman amincewar karbo irin wannan bashin ba.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀