• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA’A BUDE MAKARANTUN KIMIYYA DA FASAHA GUDA 6 – JAHAR KANO.

Kwamishinan ilimi na Jahar Kano Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru, ya bada umurnin bude makarantun kwankwarande wadanda akafi sani da makarantun fasaha guda shida 6 a fading jahar Kano. Kwamishinan yace hakan ya zama dole domin bawa dalibai yan ajin karshe damar daukan jarabawar NABTEB yan aji na shekara ta 2020.

Muhammad Sanusi yace umurnin bude makarantun ya biyo bayan sanyawa hannu akan takardar neman izinin bude makarantun da Gwabna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR yayi domin bawa daliban jahar kano damar daukan jarabawarsu ta karshe. Ya kara da cewa tini gwabnan ya bada umurnin biyawa gaba dayan daliban makarantun fasaha yan ajin karshe na jihar masu daukan jarrabawar ta NABTEB kudin jarrabawar. Sannan Gwabnan ya sake ba da umurnin fitarda zunzurutun kudi har naira miliyan Goma sha biyar da dubu Dari shida (#15.6M) domin ciyar da daliban a yayin zaman jarabawar, da kuma Karin wasu kudaden Naira dubu Dari takwas da sittin (#860,000) domin gudanar da makarantun guda shida da za’a bude.

Kwamishinan Ilimin yace an tanadi duk wasu kayayyakin kariyar kai domin tabbatarda bin ka’idodin da hukumomin lafiya suka gindaya domin kare yaduwar cutar korona acikin al’umma.

A karshe, Muhammad Sanusi Sa’id Kiru ya umurci maga-takardar ma’aikatar ilimin ya kira daraktoci/shuwagabannin makarantun da abin ya shafa a karkashin ma’aikatar makarantun kimiyya da fasaha domin wasu tsare-tsaren don cimma manufar bude makarantun.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ZA’A BUDE MAKARANTUN KIMIYYA DA FASAHA GUDA 6 – JAHAR KANO.”
  1. Hello! I just want to give you a huge thumbs up for the excellent info
    you have got right here on this post. I’ll be coming back to your blog
    for more soon.

Leave a Reply

Your email address will not be published.