• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA MU YI DIRAR MIKIYA KAN MASU KAWO FITINA A NAJERIYA-SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi alwashin dirar mikiya kan masu tada fitina a sassan Najeriya ta hanyar kisa da kona dukiyar gwamnati.

Shugaban ya baiyana haka ne a lokacin da ya ke karbar rahoto daga shugaban hukumar zabe na kona ofisoshin hukumar da ‘yan ta’addan awaren Biafra su ka yi.

Shugaban ya ce ba da dadewa ba masu tada fitinar za su sha mamaki don gwamnati za ta yi maganin su.

Ga masu buga gangar yaki, shugaban ya ce masu wannan karambani ba su san illar yaki ba ne shi ya sa su ke marmarin a gwabza.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.