• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA MU YI AIKI TARE DA HUKUMAR KASUWANCI TA RUWA WAJEN NEMAN RAGE HARAJIN ZUBA JARI A NAJERIYA – YEWANDE SADIKU “NIPC”

ByYusuf Yau

Oct 8, 2020 , ,

Shugabar hukumar bunkasa zuba jari a Najeriya Yewande Sadiku ta ba da tabbacin aiki da hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa wajen samun rage haraji don kara jawo hankalin masu zuba jari su cigaba da shigowa Najeriya, hakanan ‘yan kasa ma su samu damar kafa harkokin kasuwanci.

Yewande Sidiku na magana ne lokacin da shugaban hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa da mukarraban sa, su ka ziyarci hukumar don neman aiki tare tsakanin hukumomin gwamnati da kalubalen rashin sa kan sa hukumomin su rika aiki daban-daban ko zaman ‘yan marina.

Duk da hukumar bunkasa zuba jarin ba ta da hurumi kai tsaye na rage haraji, amma Yetunde ta ce duk bukatar hakan za ta turawa hukumomin da lamarin ya shafa musamman wani kwamiti a ma’iakatar kudi don samun ragin da ma wani lokacin yafe harajin shigo da kaya ga masu zuba jari don su kara karfi kafin a fara cin moriyar ribar su.

Shugaban hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa Hassan Bello ya ce hatta wasu masu zuba jari da a ke ce sun fice daga Najeriya za su dawo don girman kasuwar da ke Najeriya.

Hakanan Bello ya ce kamfanonin dakon kaya na jiragen ruwa na turai da su ka kara farashin dakon da kashi 400% sun rage kudin da su ka sha matsin lamba.

Hassan Bello ya kara da cewa hukumar sa na shirin kafa tashar teku ta tudu a Ibadan da za ta lashe dala miliyan 100 daga masu zuba jari don rage cunkuson tashar bakin teku ta Apapa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.