• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA MU TALLAFA WAJEN GINA GAZA AMMA ZA MU KAUCEWA TAIMAKON HAMAS-AMURKA

Sakataren wajen Amurka Anthony Blinken ya ce Amurka za ta taimaka wajen sake gina sassan birnin Gaza da ruwan boma-boman Isra’ila ya ruguza; amma za ta kaucewa taimakon ya isa ga kungiyar Hamas wacce Amurka ke dauka da kungiyar ta’addanci alhali Palasdinawa na daukar Hamas da zama garkuwar su.

Blinken wanda ke rangadi a birnin Kudus, ya ce Amurka za ta taimaka wajen farfado da Gaza da ke cikin tsarin salama da Isra’ila da ta share kwana 11 ta na zuba wuta kan Gaza da sunan karya lagon ‘yan Hamas.

Amurka za ta kaddamar da karamin ofishin jakadancin ta a birnin Kudus da tayin kulla kawance da Palasdinawa.

Abu mawuyaci a ce wata kasa za ta agazawa Gaza da yin biris da Hamas din da ke jagorantar birnin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.