• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA MU IYA BA DA GUDUNMAWA WAJEN INGANTA TSARO DON MUN IYA LIKIMO-MASU BUKATA TA MUSAMMAN

Kungiyar masu bukata ta musamman a Najeriya ta ce ‘yan kungiyar na bukatar a dauke su aiki a matsayin mashawarta a kan lamuran tsaro don sun iya likimo don gano masu aikata laifi.

Bayan ganawa a Abuja, shugaban kungiyar Yarima Sulaiman ya ce matukar jami’an tsaro sun ba su dama, za su ga sauyi wajen bankado miyagun iri da kan fake cikin al’umma su aikata miyagun laifuka.

Yarima Sulaiman ya zaiyana masu bukata ta musamman sun hada da makafin ido, guragu, kurame, bebaye da sauran su.

Kungiyar ta ba da shawara ga duk rundunonin tsaro su gwada ‘yan kungiyar ko ta hanyar daukar su masu samar da labarun sirri ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *