• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA MU HANA WASU MUNANAN DABI’U A WAJEN MAULIDI-JAM’IYYATU ANSARUL DIN ATTIJJANIYYA

ByHassan Goma

Oct 27, 2021

Reshen Najeriya na kungiyar Ansaru Din Attijjaniyya da shehun Tijjaniyya Ibrahim Nyas ya kafa da kan sa ya dau alwashin hana miyagun dabi’u da masu maulidi ke yi da hakan ke kawo kaucewa hanyar taron da sufaye ke yi duk shekara.
Kungiyar bisa jagorancin Khalifan Tijjaniyya Sunusi Lamido Sunusi ta ce daga badi za ta dau matakan kula da masu gudanar da maulidi don tantance masu yi yanda tsarin na sufaye ya ke da masu shigo da wasu dabi’u na rashin mutunci.
Babban sakataren kungiyar Alkassim Yahaya Yawuri ya nuna takaicin wani faifan bidiyon da a ka yada inda wani ke cewa ko Manzon Allah bai amince a yi maulidi ba shi sai ya yi.
Yawuri ya ce za ka ga wasu na zarmewa da furta kalmomin da za su iya fitar da su daga Islama.
Sufin na Ansaru ya ce hakanan bai zama adalci su kushe wanda ba ya fitowa ya yi jerin gwano a lokacin maulidi da a ke gudanarwa a ranar 12 ga watan rabi’ul auwal.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.