• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA MU FARA ASSASA TSANGAYAR ILIMIN LIKITA A AIKIN GININ JAMI’AR ASSALAM

Shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce aikin gina jami’ar ASSALAM mallakar kungiyar zai fara da gina tsangayar ilimin likitanci don muhimmancin aikin likita, jami’an jinya da sauran ilimin sassan kiwon lafiya ga al’umma.

Shugaban na magana ne a taro da shugabannin kungiyar na kasa da kwamitin aikin kafa jami’ar a masarautar Hadeja da ke jihar Jigawa.

Shugaban ya ce za a za a kuma cigaba da gina cibiyoyin dukkan nau’o’in ilimi don jami’ar ta amsa sunan na jami’ar duniya.

Shugaban ya kara da cewa asusun ba da gudunmawa na dukkan jama’a na bude kuma a na cigaba da taimakawa don gudanar aikin ba dare ba rana.

Sheikh Bala Lau ya ce jama’a na kishirwar samun gagarumar jami’a don samun ilimi mai amfani a duniya da gobe kiyama.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “ZA MU FARA ASSASA TSANGAYAR ILIMIN LIKITA A AIKIN GININ JAMI’AR ASSALAM”
  1. Hello, I would like to subscribe for this weblog to get hottest updates, therefore where
    can i do it please help.

  2. Hi there! This post couldn’t be written any better! Reading through this post reminds me of my previous room mate!
    He always kept chatting about this. I will forward this write-up
    to him. Pretty sure he will have a good read. Thanks for sharing!

Leave a Reply

Your email address will not be published.