• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA MU DAU MATAKAI DON KARE DALIBAI DAGA CUTAR ANNOBA-JAMI’AN MAKARANTU MASU ZAMAN KAN SU

Daidai lokacin da makarantu ke shirin komawa makaranta a litinin din nan, ma’abota makarantu masu zaman kan su, sun baiyana shirin daukar matakai masu tsauri don kare dalibai daga cutar korona.

Jami’an na cewa gwamnati ta ba su dama su cigaba da aikin su, don rufe makarantun na barazana ga sassa masu zaman kan su.

Wannan na faruwa ne daidai lokacin ministan ilimi Adamu Adamu ya jefa shakku kan bude makarantun na gwamnatin taraiya don yanda cutar annoba ke kara yaduwa, duk da daga bisani ya janye shakkun.

Shugaban kungiyar masu makarantun sakandare da firamare masu zaman kan su, Yomi Otubela ya ce ba za su iya cigaba da barin makarantun a rufe ba don zai shafi wanzuwar makarantun.

Makarantun firamare da sakanadare a wasu jihohi na gwamnati da masu zaman kan su sun koma makaranta tun farkon makon nan mai karewa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.