• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA MU DAGE DAKATAR DA TWITTER KAN WASU SHARADDA – ONYEAMA

Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce gwamnatin Najeriya za ta dage dokar dakatar da aiki da twitter in kamfanin ya dau matakin hana masu labarun tunzura jama’a da ke neman wargaza Najeriya.

Onyeama ya ce lalle sai kamfanin twitter da dau wannan mataki kafin gwamnatin Najeriya ta dage dakatarwar.

Gwamnatin dai ta kira jakadun Amurka da Burtaniya da su ka fitar da sanarwar rashin dacewar hana mutane amfani da kafofin sadarwar yanar gizo.

Gwamnatin ta ce ba wai ta na zargin twitter da kulla makirci ga Najeriya ba ne, amma ta ns tuhumar kamfanin da barin miyagun iri su na amfani da kafar wajen yada kamfen din neman raba Najeriya don kafa kasar Biafra.

Ba mamaki abun da ya kara ba wa gwamnatin takaici shi ne sakon twitter na nuna bai san Buhari ko kasar da ya ke jagoranta ba, amma ya ga sako ne na tunzura yaki don haka ya goge.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.