• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA MU BUDE TIWITA A ‘YAN KWANAKI KALILAN-LAI

Ministan labarun Najeriya Lai Muhammed ya ce gwamnatin Najeriya za ta bude aikin kamfanin tiwita da ta dakatar nan da ‘yan kwanaki kalilan.

Lai Muhammed na amsa tambaya daga manema labaru kan tiwita bayan kammala taron majalisar zartarwa na mako-mako da shugaba Buhari ya jagoranta.

Ministan ya ce tattaunawa ta yi nasara tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin sadarwar na yanar gizo.

Ministan dai ya nace wajen nuna nan ba da dadewa ba za a dage dakatarwar don masu kishirwar shiga tiwita ba zagaye-zagaye su samu damar yin hakan.

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da tiwita bayan goge wani sako na shuagba Buhari kan matakin ba sani ba sabo kan ‘yan awaren Biyafara.

Gwamnatin ta bukaci kamfanin ya yi rejista da hukumomin Najeriya da kuma daukar wani wakilin Najeriya a majalisar gudanarwar kamfanin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.