• Fri. Sep 30th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA MU BIYA MAFI TALAUCIN MUTANE NAIRA DUBU BIYAR-BIYAR DUK WATA IN MUN CIRE TALLAFIN MAI-SHAMSUNA

ByYusuf Yau

Nov 24, 2021

Ministar kudin Najeriya Zainab Shamsuna ta ce gwamnati za ta shiga turawa talakawan talak naira dubu biyar-biyar duk wata idan ta kammala janye dukkan tallafin man fetur.
Gwamnatin Najeriya na shirin janye dukkan tallafin zuwa tsakiyar shekarar badi.
Zainaba Shamsuna ta ce don rage kuncin da za a samu, gwamnati za ta rika turawa talakawa miliyan 30-40 naira dubu biyar-biyar a wata a matsayin tallafin sufuri.
Ministar ta ce gwamnati na kashe tiriliyoyin naira duk shekara don ba da tallafin, wanda hakan na da matukar illa ga aljihun gwamnati.
‘Yan kasa dai sun fi son a bar tallafin don ya zama shi ne kadai hanyar da talakawan ke amfana daga arzikin man fetur.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.