• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA A TURA MUKADDASHIN BABBAN SUFETO AYABADE DA KWAMISHINONI 8 DON ZABEN EDO

ByNoblen

Sep 12, 2020

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya tura mukaddashin sa DIG Adeleye Olusola Oyabade, mataimakin sa AIG Karma Hosea Hassan da kwamishinonin ‘yan sanda 8 don kula da tsaro a zaben gwamnan jihar Edo.
Za a gudanar da wannan zabe ranar asabar mai zuwa 19 ga watan nan nan na satumba.
Kazalika babban sufeton ya haramtawa duk jami’an tsaron da ke raka manyan ‘yan siyasa da fitowa da masu gidan na su a ranar zaben.
Hakanan sufeton ya hori duk ‘yan siyasa su tabbatar da bin doka da oda don kaucewa fadawa hushin jami’an ‘yan sandan.
Wannan dai ya nuna rundunar ta dau matakin tsaro mai tsaurin gaske kan wannan zabe da manyan jam’iyyu ke kalubalantar juna wajen neman darewa kujera.
Hakika lashe wannan kujera zai kara haska yanda babban zaben Najeriya na 2023 zai iya kasancewa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI๐Ÿ˜€๐Ÿ˜€๐Ÿ˜€
2 thoughts on “ZA A TURA MUKADDASHIN BABBAN SUFETO AYABADE DA KWAMISHINONI 8 DON ZABEN EDO”
  1. Hi my friend! I wish to say that this article is awesome, nice written and come with almost all important infos. I would like to see more posts like this .

  2. This blog is definitely rather handy since Iโ€™m at the moment creating an internet floral website โ€“ although I am only starting out therefore itโ€™s really fairly small, nothing like this site. Can link to a few of the posts here as they are quite. Thanks much. Zoey Olsen

Leave a Reply

Your email address will not be published.