• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA A SAN MATSAYAR KUNGIYAR MALAMAN JAMI’AR NAJERIYA KAN BARAZANAR YAJIN AIKI A LITININ DIN NAN

ByNoblen

Feb 14, 2022

A na sa ran sanin matsayar kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU kan barazanar yiwuwar aukawa gagarumin yajin aiki a litinin din nan.
Kungiyar malaman a taron da ta gudanar a jami’ar taraiya da ke Lagos, ta baiyana cewa za ta baiyana matsaya ta aukawa yajin ko sake ba da wata sabuwar dama ta sulhu da gwamnati.
ASUU na nuna damuwa kan zargin da ta ke yi wa gwamnati na rashin cika yarjejeniyar sulhun da ta sa a ka janye yajin aikin da ya fi kowanne dadewa a tarihi na tsawon wata tara a shekara ta 2020.
Rahoton ya baiyana cewa kungiyar za ta gudanar da taron a wani waje da ba za ta baiyana ba don gudun kar a fallasa abun da za ta aiwatar gabanin daukar matakin karshe.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.