• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

ZA A MURKUSHE’YAN TA’ADDA NAN BA DA DADEWA BA-SHUGABA BUHARI

ByNoblen

Jan 23, 2022

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa za ta murkushe ‘yan ta’adda nan ba da dadewa ba.
Mai timakawa shugaban kan labaru Garba Shehu ya ruwaito shugaban ya baiyana haka ne a karramawar da a ka yi ma sa a yayin ziyarar kaddamar da aiyukan da gwamna Nasir Elrufai ya gudanar a jihar.
Shugaban ya yabawa gwamnatin jihar ta Kaduna kan yanda ya nuna ta na taimakawa jami’an tsaro wajen inganta lamuran tsaro.
A nan shugaba Buhari ya nuna muhimmancin hadin kai rassan gwamnati wato tsakanin taraiya da jihohi wajen samar da tsaro da zaman lafiya a kasa.
Yayin da shugaban ya ke nuna farin cikin ya ziyarci Kaduna inda ya kaddamar da aiyukan raya kasa, ya baiyana fatar cigaba da kaddamar da irin wadannan aiyuka.
Shugaban ya buga misali da kaddamar da kamfanin nan na kayan abinci na OLAM ta hanyar zuba jari daga ketare da kuma ruwan Zaria.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *