Shirye-shirye sun kammala don gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Gambia a asabar din nan inda ‘yan takara 15 ke cikin sahun takarar.
Wannan ya nuna shugaban kasar Adama Barrow da ke gama wa’adin shugabancin shekaru 5, zai zage damtse don tunkarar wadannan ‘yan takarar.
In za a tuna Barrow ya zama shugaba bayan matakan da shugabannin Afurka su ka dauka na tilastawa tsohon shugaban kasar Yahaya Jammeh ya sauka daga mulki bayan shank aye a zaben da Barrow ya samu galabar.
Har yanzu a na ganin Jammeh na da tasiri a lamuran siyasar Gambia duk da a na hasashen gudanar da zaben a tsanake.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀