• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA A GUDANAR DA ZABE A KARAMAR HUKUMAR IHIALA A TALATAR NAN KAFIN AIYANA SAKAMAKO

ByYusuf Yau

Nov 9, 2021

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce za ta gudanar da zabe a karamar hukumar Ihiala da ke jihar Anambra kafin aiyana wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Hukumar ta ce ba ta iya gudanar da zabe a karamar hukumar ranar asabar da a ka tsayar don yin zabe a dukkan jihar ba.

Jami’ar aiyana sakamakon zabe ta jihar Florence Obi ta baiyana cewa saboda da barazana, hukumar ba ta samu gudanar da zaben ba kuma doka ta yi umurnin sai an gudanar da zabe a dukkan kananan hukumomin jihar kafin aiyana wanda ya kashe zabe.

Za a gudanarvda zaben a mazabu 326 na karamar hukumar ta Ihiala.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.