• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ZA A BADA LADAR DALA MILIYAN 10 GA WANDA YA GANO WANDA YA KASHE RAFIK HARIRI NA LEBANON

ByNoblen

Mar 30, 2021 ,

Amurka ta aiyana ware ladar dala miliyan 10 ga duk wanda ya ba da labarin yanda za a cafke wanda a ka tabbatar shi ya kitsa kisan gilla ga marigayi firaministan Lebanon Rafik Hariri.

Kotun dai ta samu Salim Ayyash da laifin hari kan kwambar motocin da Hariri ya ke ciki inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar sa da wasu mutane da dama a 2004.

Amurka za ta ba da ladar kazalika ga duk bayanin da zai kai ga dakile Ayyash daga kai hari kan Amurka ko muradun Amurka.

Ayyash dai don kungiyar ‘yan shia ta Hezbollah ne kuma kungiyar ta na ba shi kariya don hana shi fuskantar hukuncin da a ke yanke ma sa.

An tabbatar Ayyash mai shekaru 57 na boye a Lebanon inda shugaban Hesbollah Hassan Nasrallah ya ki mika shi ga kotun ta musamman ta majalisar dinkin duniya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *