• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YUNKURIN JUYIN MULKI A SUDAN DAGA JAMA’AR TSOHON SHUGABA OMAR ELBASHIR NE-HUKUMOMIN KHARTOUM

ByNoblen

Sep 22, 2021 , ,

Hukumomin gwamnatin rikwan kwaryar kasar Sudan sun ce yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba daga tsohuwar gwamnatin shugaba Omar Elbashir ne.
Firaministan kasar Abdalla Hamdok ya baiyana haka da nuna cewa yunkurin manuniya ce ta yanda lamura su ka rikice a kasar da ke kokarin komawa tsarin dimokradiyya.
Ministan labarun kasar Hamza Baloul ya ce an shawo kan yunkurin kuma wadanda ke cikin lamarin da su ka hada da sojoji da farar hula an kama su.
Jami’an tsaro sun rufe gadar da ta ratsa kogin nilu ta hade babban birnin kasar da birnin Omdurman.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *