• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YUNKURIN HOUTHI NA MAIDA JAKADAN IRAN GIDA YA JAWO MUHAWARA A SANA’A

ByNoblen

Dec 19, 2021 , ,

Yunkurin da ‘yan tawayen houthi a Yaman su ka yi na neman maida jakadan Iran a babban birnin kasar Sanaa, ya jawo muhawara tsakanin masu ganin matakin ya dace da masu tunanin akwai alamun an samu rashin jituwa. dangantaka tsakanin kasashenbiyu.
Iran ke marawa kungiyar ‘yan tawayen baya ta hanyar makamai har ta kori gwamnatin kasar daga zama a babbar birnin kasar a 2014.
Ba mamaki wasu na daukar jakadan Hassan Erlo a matsayin wanda ya karbe ragamar jagorancin aiyukan ‘yan houthi wajen yakar gwamnatin kasar ta Abed Rabbo Mansour Hadi.
Masu fashin bakin siyasar sun ce ba yanda za a yi houthi ta samu rugujewar dangantaka da Iran.
Mai ba wa shugaban Yaman shawara Yassen Makkawi ya ce houthi kungiyar mayaka ne da Iran ke amfani da ita wajen wargaza zaman lafiya a yankin gabar ta tsakiya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *