• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

YUNKURIN HANA SIMOGA A LEBANON YA JAWO GAGARUMAR ZANGA-ZANGA

ByNoblen

Jun 22, 2021 ,

Yunkurin jami’ai a Lebanon na hana simoga ya jawo gagarumar zanga-zanga da kona tayu a kan iyakar Lebanon din da Sham.

Lamarin ya taso biyo bayan yunkurin datse masu simogar gas daga Lebanon zuwa Sham don ratsawa ta hanyar Masnaa da a ka amince wajen shiga Sham.

Tsadar rayuwa a Lebanon ta sa wasu kan cika motocin su da kayan masaarufi da fetur su shige cikin Sham inda su ke cin riba ninki biyu daga farashin kasar su.

Jarkar fetur mai daukar lita 20 na kai wa dalar Amurka 29 a Lebanon nan ma sai an bi dogon layi saboda yanda lamura su ka tabarbare a kasar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *