Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya jagoranci taron majalisar zartarwa wanda a kan gudanar a fadar Aso Rock.
Osinbajo ya yi jagorancin ne don shugaba Buhari ya kai ziyarar aiki kasar Spain bisa gaiyatar shugaban kasar Pedro Sanchez.
Sakataren gwamnati Boss Mustapha da shugaban ma’aikatar fadar Ibrahim Gambari da ministoci da dama sun halarci taron.
Osinbajo dai na daga masu neman takarar shugabancin kasa a inuwar APC.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀